1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na ci gaba da kamen 'yan adawar kasar

Binta Aliyu Zurmi
July 1, 2025

Jami'an 'yan sandan kasar Turkiyya sun kama sama da mutane 120 a birnin Izmir da ke zama wata tungar 'yan adawa tsawon shekaru.

Türkei Istanbul 2025 | Polizei sichert einen Protest gegen die Satirezeitschrift LeMan ab
Hoto: Francisco Seco/AP/picture alliance

Hakan na zuwa ne sa'o'i kafin wani muhimmin gangami a birnin Santanbul da nufin yin tir da matakin ci gaba da yi wa 'yan adawa dauki dai-dai da gwamnatin Ankara ke yi.

Wannan kamen wani bangare ne na binciken zargin cin hanci da rashawa da aka yi a zauren majalisar dattijai dake Izmir, ya kuma biyo bayan wani samame da aka yi a Santanbul karkashin ikon ‘yan adawa a watan Maris, wanda ya kori magajin garin Ekrem Imamoglu, babban abokin hamayyar siyasar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta CHP, Murat Bakan, ya ce tsohon magajin gari da manyan jami'ai da dama na daga cikin wadanda ake tsare da su a birnin Izmir, 

Ofishin mai shigar da kara na Izmir ya bayar da sammacin kama mutane 157, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Karin Bayani: Turkiyya ta kama daruruwan masu boren kin jinin gwamnati