'Yan Sanda sun farma masu adawa da shugaban Senegal
February 1, 2012'Yan sandan kwantar da tarzoma a birnin Dakar na ƙasar Senegal sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar nuna adawa da shugaban ƙasar. Dubbannin 'yan ƙasar Senegal ne dai suka yi gangamin nuna adawa da hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta Senegal ta yanke na baiwa shugaba Abdoulaye Wade damar tsayawa takara a wa'adi na ukku domin ci gaba da shugabancin ƙasar a zaɓukan da za'a gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairun nan - idan Alah ya kaimu.
Jim kaɗan bayan da shugaba Wade ya ɗare bisa kujerar shugabancin Senegal ne ya canza tsarin mulkin ƙasar, tare da baiwa shugaban ƙasa damar tsayawa takara na wa'adi biyu. Sai dai kuma a baya bayannan ne kotun ƙolin ƙasar ta Senegal ta yanke hukuncin cewar tanadin zai yi aiki ne akan shugabannin da za su zo nan gaba, amma banda shugaba Wade, wanda shekarun sa na haihuwa 85 ne a duniya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal