1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wadanda suka yi wa likita fyade

Ramatu Garba Baba
December 6, 2019

'Yan sanda sun harbe wasu mutum 4 a yayin gudanar da bincike kan zargin da ake musu na kisan wata likitar dabbobi bayan da suka yi mata fyade.

Indien Pakistan Symbolbild Vergewaltigung
Hoto: Getty Images

Matakin da 'yan sanda a kasar Indiya suka dauka na harbe wasu mutane hudu da ake zargi da yi wa wata Likitar dabbobi fyade kafin su kashe ta, ya janyo ra'ayoyi mababanta a kasar. A dai safiyar wannan Jumma'ar ce, fada ya barke a tsakanin jami'an 'yan sandan da wadanda ake zargin bayan da suka yi yunkurin kwace makamai daga hannunsu, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake binciken tabbatar da laifin a kan matasan.


N Prakash Reddy shi ne mukaddashin 'yan sandan birnin Hydrabad da ke jagorantar binciken, ya ce, akwai jami'ansu biyu da suka ji rauni a yayin hatsaniyar. Babu dai cikakken  bayani daga mahukunta kan yawan jami'an tsaron da ke rakiyar masu laifin a yayin da rikicin ya barke. Iyalan matar mai shekaru 27 da haihuwa dama sauran al'umma musamman wadanda ke hakilon ganin an kawo karshen cin zarafin mata sun nuna gamsuwarsu, a yayin da wasu ke ganin bai dace 'yan sandan su dauki doka a hannunsu ba.


Matsalar fyade da ake yi wa mata a Indiya, na ci gaba da jan hankulan kungiyoyi masu rajin kare hakkin mata ba tare da an iya shawo kanta ba. A shekarar 2017 kadai, mata sama da dubu talatin da biyu aka yi wa fyade a Indiya.