'Yan sanda sun kama jagoran adawa a Rasha
May 5, 2018Talla
A cewar kafafan yada labarai na Rasha an kama dan adawar ne ana tsakiya da gangamin adawar da ya samu halartar dubban masu adawa da shugabancin Putin.
A cewar wani jami'i da ke aiki tare da Navalny dubban mutane ne za su fita zanga-zangar a birane 90 a fadin kasar don nuna adawa da sake zaben shugaban na Rasha a karo na hudu, inda shugaban zai rantsuwar kama aiki a ranar Litinin. 'Yan sanda sun kama mutane sama da 300 a fadin kasar bayan fitarsu wannan zanga-zanga a cewar 'yan fafutika.