'Yan sanda sun kashe dan Najeriya a Afrika ta Kudu
September 6, 2017Talla
A wata sanarwa da ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Najeriya ya fitar ta ce mutunen dan shekaru 27 da haihuwa mai suna Kingsley Ikeri, ya gamu da ajalinsa ne bayan da 'yan sandan Afirka ta Kudu suka gana masa azaba a yankin Kwazulu-Natal, inda sanarwar ta ce 'yan sandan na tuhumarsa ne da fataucin miyagun kwayoyi.
Tuni dai karamar Ministar harkokin wajen ta Najeriya Ifeoma Akabogu Chinwubab ta nuna bacin ranta ga wannan mataki na 'yan sandan kasar ta Afirka ta Kudu, inda ta nemi hukumomin kasar da su gurfanar da wadannan 'yan sanda a gaban kuliya ba tare da bata lokaci ba.