1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abuja: 'Yan sanda sun mutu a rikicin Shi'a

Abdul-raheem Hassan
August 25, 2024

Lamarin ya faru ne yayin da mabiya kungiyar IMN ke tattakin 'Arbaeen' wanda suka saba yi na cika kwanaki 40 bayan Ashura. 'Yan sanda sun zarge su da farwa ababen hawansu a shingen bincike.

Mabiya Shi'a na tattaki a Najeriya
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami'anta guda biyu wasu guda uku sun samu mumunar rauni tare da kona motocin 'yan sanda a wani rikici da ya barke tsakaninsu da 'yan Shi'a a Abuja babban birnin kasar.

"Haramtacciyar kungiyar ta kai hari a shingen bincike, suna dauke da adduna da wasu ababen fashewa da wukake,” inji mai magana da yawun ‘yan sandan Josephine Adeh a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Rundunar ta ce an kama mutane da dama, inda kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja CP Benneth C. Igweh, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu. Mabiya kungiyar IMN na gudanar da jerin gwano da suka saba yi na cika kwanaki 40 bayan Ashura.

Tun a shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar Shi'a ta IMN, bayan wata zanga-zangar neman a saki shugabanta Sheik Ibrahim El-Zakzaky da aka daure tun a shekarar 2015 zuwa 2021 bayan artabu da sojoji wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 300.