An yi boren adawa da zaben Aljeriya
December 12, 2019![Algerien pro-Regierungsprotest in Algiers](https://static.dw.com/image/51485069_800.webp)
Talla
'Yan sadan sun watsar da taron masu zanga-zanga da suka fara taruwa a babban wurin taro da masu boren ke haduwa domin adawa da gwamnati.
'Yan takara biyar ke fafatawa a zaben domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, sai dai 'yan kasar na Allah wadai da daukacin 'yan takara a zaben, inda suke alakantasu da tsohon shugaban.