Yan adawa a Ghana sun yi zanga-zanga
December 17, 2020Talla
'Yan adawar sun yi gangamin ne domin nuna kin amincewa da sakamakon zaben da hukumar ta bayyana wanda ta tabbatar cewa Nana Akufo Addo shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar tara ga watan Disamba, da kishi 51,59 a gaban dan takarar jam'iyyar adawa John Mahama da ke dashi 47.36. Jami'an tsaron na Ghana sun kama da yawa daga cikin shugabannin adawar da suka jagoranci gangamin.