'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Benin
April 27, 2024Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana cewa 'yan sanda sun tarwatsa wasu gungun mutanen da ke gudanar da zanga-zangar a babban birnin kasar.
Karin bayani: Jamhuriyar Benin ta sake bude kofofinta ga 'yan Nijar
Kazalika guda daga cikin masu zanga-zangar Ariane Assilamehou ta shaidawa AFP cewa 'ta zo ne domin shiga gangamin yaki da tsadar rayuwa, amma 'yan sanda sun hana su rawar-gaban hantsi wajen harbin su da barkonon tsohuwa.
Karin bayani: Benin ta janye haramcin da ta yi wa Nijar na fiton kayayyakinta ta gabar ruwan Cotonou
Babbar kungiyar kwadagon kasar ta Benin CSA ta ce 'yan sanda sun yi awon-gaba da shugaban kungiyar Anselme Amoussou. 'Yan sanda sun ki cewa uffan dangane da wannan al'amari na murkushe masu zanga-zangar tsadar rayuwa a gwamnatin shugaba Patrice Talon.