1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takun saka a siyasar Guinea Bissau

Suleiman Babayo USU
December 13, 2023

A birnin Bissau fadar gwamnatin kasar Guinea-Bissau 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye domin tarwatsa 'yan majalisar dokokin da aka rusa da suka yi yunkurin sake haduwa.

'Yan sanda sun tarwatsa 'yan majalisar dokokin Guinea-Bissau da aka rusa da suka yi yunkurin sake haduwa
'Yan sanda sun tarwatsa 'yan majalisar dokokin Guinea-Bissau da aka rusa da suka yi yunkurin sake haduwaHoto: Alison Cabral/DW

'Yan sanda a birnin Bissau fadar gwamnatin kasar Guinea-Bissau sun watsa hayaki mai saka hawaye domin tarwatsa 'yan majalisa na bangaren adawa wadanda suka yi yunkurin haduwa duk da matakin Shugaba Umaro Sissoco Embalo na rusa majalisar.

A makon jiya shugaban kasar ya rusa majalisar wadda 'yan adawa suka mamaye, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi inda aka samu harbe-harbe.

Karkashin dokokin kasar ta Guinea-Bissau da ke yankin yammacin Afirka, bangaren da yake da rinjaye a majslair dokoki yake nada jagororin gwamnati amma shugaban kasa yana da ikon rusa majalisar dokokin.