Dan adawar Zambiya na hannun 'yan sanda
August 27, 2026
Jami'an 'yan sanda a Zambiya sun sanar da kama madugun 'yan adawan kasar Brian Mundubile, inda suke yi masa tambayoyi biyo bayan hargitsin da ya barke a zaben shugaban kasar da a gudanar a makon jiya.
Zambia ta dakatar da sanar da sakamakon zabe
Gidan rediyon kasa na Zambiya, ya ce Mundubile da mutumin da ya yi masa takarar mataimaki Makebi Zulu sun shiga hannun hukuma, suna kuma yi musu tambayoyi.
Kakakin hukumar 'yan sandan Zambiya Godfrey Chilabi, ya sanar da cewar an saurari bayanai daga jagoran na 'yan adawa, game da zanga-zangar kin jinin sakkamakon zabe da ta barke a washe garin ranar zaben da babbar jam'iyyar da ke mulkin kasar ta yi nasara, sannan kuma za a fitar da sanarwa idan an kammala yi masa tambayoyi.
Yan Zambia sun yi zaben shugaban kasa
Mutum guda ne dai ya ce gagrinku, a yayin 'yan sanda suka cika hannu da membobi da dama na jam'iyyar ta madugun 'yan adawar, bisa boren kin jinin sakamakon da suka nuna a rranar 13 ga wannan Agusta.
Hukumomin Zambiya sun bayyana shugaba Hakainde Hichilema a matsayin wanda ya lashe zaben, duk da cewa an samu takaddama kan sakamakon.