'Yan sanda sun yi artabu da masoyan Messi a Indiya
December 13, 2025
Daruruwan masoyan dan wasan sun sanya da rigarsa tare da rera wakar girmama shi, wasu kuma sun fusata sun fasa alluna da kayan adon da aka tsara a filin saboda jami'an tsaro sun hana su shiga farfajiyar dukd a cewa sun sayi tikiti da kudi mai tsada da iyalansu don su yi ido hudu da tauraron dan wasan.
"A gare ni, kallon Messi abin farin ciki ne, mafarki ne. Amma na rasa damar da zan iya tabbatard a mafarkin saboda rashin tsarin gudanarwa mai kyau." a cewar wani dan kasuwa Nabin Chatterjee, mai shekaru 37.
Wasu da dama sun sayi tikitin sama da dala 100 don wannan rana. "Na biya Rs 5,000 kwatankwacin da 55 na tikitin kuma na zo da dana don kallon Messi, ba 'yan siyasa ba, 'yan sanda da sojoji suna daukar hotun selfie, kuma masu gudanarwa ne ke da alhakin," Ajay Shah wani masoyin Messi.
An ga yadda 'yan siyasa suka yi ta rige-rigen daukar hotuna da dan wasan, yayin da dimbin masoyansa me ke nuna sha'awar daukar hotuna tare da shi. Dandalin ya rikide zuwa tarzoma a lokacin da masoya suka fara jefin 'yan sanda da kwalabe, matakin da ya tilasta fitan dan wasan da wuri daga dandalin.
Aved Shamim, wani babban jami'in ‘yan sanda a jihar, ya shaida wa manema labarai cewa, an kama babban mai shirya taron, ba tare da yin wani karin bayani ba. Linoel Messi mai shekaru 38, na rangadin kwanaki uku a Hyderabad da Mumbai da kuma New Delhi inda ake sa ran zai gana da Firaiministan Indiya Narendra Modi, a wani bangare na yawon ganawa da masoyansa a mastayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na wannan zamani.
Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi kowa daraja a gasar Major League Soccer a karo na biyu a jere a wannan makon, bayan da ya akalar Inter Miamilashe gasar MLS kuma shi ya fi yawan kwallaye a gasar.
Tsohon dan wasan na Barcelona da Paris Saint-Germain, zai jagoranci kasarsa Argentina karekofin duniya da ke hannunta a gasar da za a fara a watan Yuni zuwa Juli a Arewacin Amurka.