1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciTurai

'Yan sandan Brussels na neman wanda ya yi kisa ruwa a jallo

Mouhamadou Awal Balarabe
October 18, 2023

Bayan harin da aka kai kan wasu 'yan kasar Sweden biyu a birnin Brussels na Beljiyam, ana ci gaba da neman wanda ake zargi da kisan gilla. Hukumomi suka ce dan asalin Tunisiya ne ya dauki alhakin harin.

'Yan sanda sun killace wasu sassa na birnin Brussels bisa dalilai na tsaro
'Yan sanda sun killace wasu sassa na birnin Brussels bisa dalilai na tsaroHoto: Lou Lampaert/Belga/dpa/picture alliance

Bayan harin da aka kai kan wasu 'yan kasar Sweden biyu a birnin Brussels na Beljiyam, ana ci gaba da neman wanda ake zargi da kisan gillan ruwa a jallo. Firayiministan wannan kasa Alexander De Croo ya ce wani mutum dan asalin Tunisiya ne ya dauki alhakin harin ta yanar gizo, inda ya ce ya yi amfani da dabarun  mayakan IS wajen aikata wannan danyen aiki. Tuni ma dai aka ayyana mafi girman matakin barazanar ta'addanci ga babban birnin kasar ta Beljiyam.

Karin bayani: Ci gaba da bincike kan harin Beljiyam

A yammacin ranar Litinin ne, wani mutum dauke da makamai ya yi harbi a tsakiyar birnin. 'Yan kasar Sweden biyu ne suka mutu a kusa da filin wasan kwallon kafa na Brussels, inda 'yan wasan kasashen Beljiyam da Sweden za su fafata da juna. Amma dai an soke wasan daga bisani don gudun abin da ka je ya zo.