1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sandan Ghana sun cafke jagoran boren tsadar rayuwa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
September 24, 2024

Matasan da ke zanga-zangar sun koka da tsadar rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da yadda masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ke gurbata muhalli.

Wasu yan Ghana da ke zanga-zanga a shekarun baya
Wasu yan Ghana da ke zanga-zanga a shekarun bayaHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Rundunar 'yan sandan Ghana ta cafke jagoran masu zanga-zangar adawa da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba Oliver Barker-Vormawor, tare da wasu mukarrabansa uku, kwana guda bayan kama mutane 42 da suka yi arangama da 'yan sandan a Accra babban birnin kasar.

Karin bayani:Fargaba gabanin babban zabe a Ghana

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Ghana Grace Ansah-Akrofi, ta ce sun kama Mr Oliver Barker-Vormawor bisa aikata laifukan da suka saba wa dokokin kasar, ta inda suka far wa 'yan sanda a daidai lokacin da suke tsaka da aikinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Karin bayani:Cece-kuce gabanin zaben shugaban kasar Ghana

Zanga-zangar wadda kungiyar nan mai rajin kare dimukuradiyya da yaki da tsadar rayuwa ta Democracy Hub ta shirya, ta barke ne a ranar Juma'ar da ta gabata sannan ta karkare a jiya Lititin.

Matasan da ke zanga-zangar sun koka matuka da yadda tsadar rayuwa ke kara kamari a kasar, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, sai kuma yadda masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ke gurbata muhalli.