1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yan sandan Jamus far wa Kurdawa yan Iraqi masu safarar baki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 4, 2024

Matakin ya biyo bayan binciken karkashin kasa da kasashen Belgium da Jamus da kuma Faransa suka gudanar, tare da kama gungun Kurdawa 'yan Iraqi.

Hoto: Leon Salner/RESQSHIP e.V./dpa/picture alliance

Daruruwan 'yan sandan Jamus sun kai samame a birane da dama na kasar, kan tungar wasu Kurdawa 'yan kasar Iraqi da ke safarar 'yan gudun hijirar yankin Gabas ta Tsakiya da Gabashin Afirka cikin kasar ba bisa ka'ida ba, ta hanyar amfani da kwale-kwale daga Faransa da kuma Burtaniya.

karin bayani:Jamus: Tantance masu neman mafaka a wata kasa

Fiye da 'yan sanda 500 na Jamus da hadin gwiwar jami'an tsaron Faransa da kuma na Turai Europol ne suka gudanar da aikin samamen a biranen Essen da Gelsenkirchen da Grevenbroich da Bochum da sauransu.

Ko da yake babu wani karin haske kan adadin mutanen da aka kama zuwa yanzu, amma ministar harkokin cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta jinjinawa aikin sintirin da jami'an tsaron suka gudanar, kan gurbatattun mutanen da ke jefa rayukan jama'a cikin hatsari tare da aikata miyagun laifuka.

Karin bayani:Jamus ta kai makura kan 'yan gudun hijira

Wannan mataki ya biyo bayan binciken karkashin kasa da kasashen Belgium da Jamus da kuma Faransa suka gudanar a farkon wannan shekara, tare da kama gungun Kurdawa 'yan Iraqi 19 da ke safarar mutane zuwa Turai ba bisa ka'ida ba.