1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan sanda sun cafke wanda ya yi garkuwa da 'yarsa a Jamus

November 5, 2023

Rundunar 'yan sandan Hamburg ta ce mutumin ya samu sabani da matarsa kan wanda ya dace ya rike ta, inda bayan sun fara sa'in'sa ne sai matar ta sa ta kira 'yan sanda domin shaida musu cewa ya yi garkuwa da 'yar su

Hoto: Martin Ziemer/Getty Images

'Yan sandan Jamus sun samu nasarar cafke wani mutum a birnin Hamburg dauke da bindiga, inda ya yi garkuwa da 'yarsa mai shekaru 4 da haihuwa a cikin mota, bayan tataburza ta tsawon sa'o'i 18 da aka sha da shi a hanyar filin jirgin saman Hamburg.

Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun gano sakon kai hari a kasar

Rundunar 'yan sandan Hamburg ta ce mutumin mai shekaru 35, ya samu sabani da mahaifiyar yarinyar kan wanda ya dace ya rike ta, inda bayan sun fara sa'in'sa ne sai matar ta sa ta kira 'yan sanda domin shaida musu cewa ya yi garkuwa da 'yar su.

Karin bayani:Jamus: Matashi ya kashe kakarsa mai shekaru 100

Tuni dai 'yan sandan suka ba da umarnin ci gaba da hada-hadar jigilar fasinjoji a filin jirgin saman Hamburg, wanda aka dakatar a baya sakamakon harbi da bindiga da mutumin ya rinka yi kafin ya mika kansa ga 'yan sandan ba tare da wata tirjiya ba.