1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan sandan Jamus na binciken 'yar ta'addar nan Daniela

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 29, 2024

'Yan sandan na zargin Klette da aikata miyagun laifukan fashi da makami da yunkurin kisan kai dga shekarar 1999 zuwa 2016, karkashin kungiyarta ta Red Army Faction wato RAF, wadda aka kafa a shekarar 1968

Hoto: Sina Schuldt/dpa/picture alliance

'Yan sandan Jamus sun sanar da kawo karshen binciken da suke gudanarwa a gidan da tsohuwar 'yar ta'addar nan Daniela Klette ta kungiyar Red Army Faction ta zauna a birnin Berlin, inda suka samu tarin makamai a Alhamis din nan.

Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun cafke wani mutum da ya yi garkuwa da 'yarsa mai shekara 4

A ranar Litinin din da ta gabata ne 'yan sandan suka kama matar mai shekaru 65, bayan ta yi badda bamin sauya suna, kamar yadda suka wallafa a shafinsu na X, sannan suka kwashe mazauna ginin baki-daya don gudanar da bincike.

Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun gano sakon kai hari a kasar

'Yan sandan dai na zargin Klette da aikata miyagun laifukan fashi da makami da yunkurin kisan kai a lokuta da dama daga shekarar 1999 zuwa 2016, karkashin kungiyarta ta Red Army Faction wato RAF, wadda aka kafa a shekarar 1968 don aikata muggan laifuka.