1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya sun cafke shugaban NLC

November 1, 2023

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke shugaban kungiyar kwago ta kasar NLC Joe Ajaero tare da yi masa dukan tsiya kafin a saka shi a cikin mota.

'Yan sandan Najeriya sun cafke shugaban NLCHoto: Uwais/DW

Manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya guda biyu sun ce an cafke shugaban na NLC Joe Ajaero a lokacin wata zanga-zangar kare hakkin ma'akaita wacce aka gudanar a jihar Imo da ke Kudu masu Gabashin kasar.

Kaarin bayani: Najeriya: Kungiyar NLC ta yi watsi da karin farashin mai

Cafke dan gwagwarmayar na zuwa ne a daidai lokacin da manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC ke tattaunawa da gwamnati kan sauyen-sauyen da kasar ta yi a baya-bayan nan ciki har da cire tallafin man fetur wanda ya haddasa tsadar rayuwa da masasarar tattalin arziki.