1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya sun ce ba su hana gangami ba

June 3, 2014

Rundunar 'yan sanda ta tarayyar Najeriya ta janye umarnin da ta bayar na haramta gangami ko zanga-zangar lumana a ko-ina cikin kasar.

Nigeria Frank Mba
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya bayar lokacin wani taron manema labarai a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ya ce rundunar ce ta bayar da shawara ne kawai ga 'yan kasar da su rinka takatsantsan wajen gudanar da gangami musammam a birnin tarayya Abuja da kewaye, saboda barazanar tsaro da kasar ke fuskanta yanzu.

Da ma tun farko 'yan kungiyar #bringbackourgirls masu fafutukar matsa lamba kan gwamnatin Najeriya ta kara azama wajen nemo 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, sun nufi kotu don kalubalantar haramcin zanga-zangar da 'yan sandan kasar suka dora kansu.

Rundunar ta jaddada bukatar masu shirya irin wannan gangami su rinka neman shawara da jagorancin rundunar kafin gudanar da irin wannan taro don kauce wa faruwar duk wani abin da bai dace ba.

Hoto: Reuters

Babu dai zato ba kuma tsammani rundunar 'yan sandan kasar ta ce ta kai ga haramci kan duk wata zanga-zangar da ke da ruwa da tsaki da bukatar ceto yaran, da suka shafe kwanaki 50 a hannun 'yan bindigar na Boko Haram.

Kwamishinan 'yan sandan birnin Ombu Josheph Ombu ya sanar da haramcin da ya tada hankula ya kuma kai 'yan kungiyar zuwa bakin kotu.

Karkashin daya a cikin manyan lauyoyin kasar Femi Falana dai masu ruwa da tsaki da tabbatar da ceto yaran dai sun nemi kotun da ta tabbatar da hakkinsu na taruwa irinta lumana, da ma baiyana ra'ayi da babu tada hankali a cikinsa.

Ba gudu ba ja da baya ga fafatuka

Sambido Hose dake zaman shugaban kungiyar mazauna Chibok da ke Abuja kuma daya a masu shirya zanga-zangar ta Abuja ya ce babu gudu babu ja da baya da zarar sun samu hukuncin kotun da ke iya bude sabon babi cikin rikicin da ke dada daukar hankali da sabo na salo.

'A yau kan mun dan dakatar amma in mun ji abun da kotu ta fada to zamu san abun da za mu yi, in kotu ta yanke a cikin gamsassun hujojji, to za mu bi umarni, in kotu ta ce ku ci gaba kafin yanke hukunci, to za mu ci gaba in kotu ta ce ku dakatar har sai an yanke shari'a to za mu dakatar.'

Hoto: picture-alliance/AP Photo

An dai share kwanaki har 50 an kuma gaiyato sojoji da makamai amma har yanzu ana kila-wa-kala ga tabbatar da gano 'yan matan na Chibok, ga shugaban kasar da ke neman hanyar kaddamar da yakin neman zabe amma kuma ke shirin fuskantar fushi na masu tunanin an kasa.

Katsalandan cikin zanga-zangar lumana

Tuni dai kotun kolin kasar ta ce ta soke ga duk wani kokari na tsoma baki na jami'an tsaron ga harkokin da suka shafi zanga-zangogi na lumana a fadar Barister Shariff Mohammed wani lauya mai zaman kansa cikin kasar da kuma ya ce an saba kuma an kai ga kauce hanya a bisa matakin 'yan sandan kasar ta Najeriya.

''Yan kwanakin da suka gabata an tafi an dauki hayar wasu sun zo wai su ma 'yan fafutukar a saki yaran Chibok ne suka farma wadannan mutane: Na kuma saurari ministan yada labarin Najeriya na cewar wai kashi 90 cikin 100 na mutanen nan 'yan wasu jam'iyyun adawa ne. In ka hada wadannan bayanai za su nuna maka cewar kokari ne gwamnati na korar mutanen nan da ke tsakiyar gari.'

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal