Saliyo ta zargi tsohon shugaban kasa da kitsa juyin mulki
December 13, 2023Rundunar 'yan sandan kasar Saliyo ta zargi tsohon shugaban kasa Ernest Bai Koroma da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 26 ga watan Nuwamban da ya gabata.
Karin bayani:An kama wanda ya kitsa juyin mulki a Saliyo
Shugaban rundunar Fayia Sellu ne ya tabbatar da hakan a Talatar nan yayin taron manema labarai a Freetown babban birnin kasar, lokacin da yake amsa tambayoyi daga ministan yada labaran Chernoh Bah.
karin bayani:ECOWAS za ta yi taro kan matsalolin juyin mulkin sojoji a yankin
Yunkurin juyin mulkin dai ya yi sanadiyyar hallaka mutane 21, da suka hada da jami'an tsaro 18 da kuma maharan guda 3, inda ya zuwa yanzu aka kama mutane 80 da ake zargi da hannu wajen shirya juyin mulkin, ciki har da dogarin tsohon shugaban kasar Bai Koroma.