1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sandan Senegal sun tarwatsa masu zanga-zanga a Dakar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 9, 2024

Tun bayan da shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben kasar ake ta fuskantar tarzoma a kasar

Hoto: GUY PETERSON/AFP

Jami'an tsaron kasar Senegal sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa wasu matasa da ke kokarin fara zanga-zanga a Dakar babban birnin kasar, don nuna fushinsu da matakin shugaba Macky Sall na dage babban zaben kasar.

Karin bayani:Siyasar Senegal da mutuwar shugaban Namibiya a jaridun Jamus

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya hango dandazon matasan suna gararanba a kan tituna, suna jifan 'yan sanda da duwatsu, a kokarinsu na isa da'irar da za taru, daga nan 'yan sandan suka harba musu hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su.

Karin bayani:Majalisa ta amince da dage zabe a Senegal

Tun bayan da shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben kasar ake ta fuskantar tarzoma a kasar.