'Yan sandan Turkiyya sun damke wani dan IS
November 12, 2015Talla
Majiyar 'yan sandan ta bayyana cewar mutum mai suna Mehdibend Sa'id, an sanya masa idanu bayan ya shiga cikin kasar Syriya a inda yake yunkurin gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar Turkiya. An dai dmnkesh ine a wani gari mai suna Izmir bayan da jami'an leken asirin yankin suka sanar da jami'an tsaro.
Jami'an tsaron Turkiyya na daukar matakan kakkabe wadanda suke da alaka da kungiyar 'yan jihadi tun lokacin da aka hallaka mutane da dama a wani harin kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Ankara na Turkiya da mayakan Is suka kai.