'Yan sandan Yuganda sun kama Bobi Wine
April 29, 2019![Uganda Pop Star l MP Robert Kyagulanyi, alias Bobi Wine](https://static.dw.com/image/48433720_800.webp)
Jami'an 'yan sandan Yuganda sun sake cafke dan gwagwarmayar nan Bobi Wine sa’o’I 48 bayan dan adawan ya samu 'yancinsa na walwala da zirga-zirga. Masu aiko da rahotanni sun ambato lauyan Bobi Wine na cewa “tun da sanyin safiya ne ‘yan sanda suka kamashi tare da tsareshi a wani ofishin ‘yan sanda da ke wajen birnin Kampala ba tare da bayyana dalilan da suka haddasa kamunsa ba. "
Dan shekaru 37 da haihuwa, mawakin Bobi Wine ya yi kaurin suna wajen caccakar masu zartar da mulki a kasar Yuganda wanda har ma matasan kasar suke daukarsa a matsayin wani jagoran juyin-juya hali domin isar da sakonsu ga mahukunta, Si dai tun a ranar 23 ga wannan watan aka girke jami’an ‘yan sanda a gaban kofarsa tare da hana hi duk wani motsin da ya shafi shige da fice.