1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraqi: 'Yan shi'a sun fusata da sabon Firaminista

March 18, 2020

Rahotanni daga Bagadaza babban nirnin kasar Iraqi na cewa jam'iyyun siyasa mallakar mabiya mazhabar shi'a a kasar sun bijire wa nadin da aka yi wa sabon Firaminista Adnan al-Zurfi.

Irak Protest
Hoto: AFP/S. Arar

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito 'yan shi'a na nuna rashin jin dadinsu a kan hanyoyin da aka bi wurin zaben Firaminitsan mai jiran-gado Adnan al-Zurfi.

Shi dai Adnan al-Zurfi mai shekaru 54 tsohon dan majalisa ne kuma tsohon gwamnan yankin Najaf a kasar ta Iraqi. Ana sa ran nadin nasa zai kawo karshen rikicin siyasa a kan wannan mukami da kasar ta shafe wani lokaci tana fama da shi. 

A gefe guda kuwa shugaban kasar ta Iraqi Barham Salih ya ce yana fata al-Zurfi zai kafa gwamnatin jama'a, inda ya kara da cewa hadin kan 'yan kasar Iraqi da zaman lafiyarsu su ne muhimman abubuwan da ke a gabansa.


A yanzu dai sabon Firaminista Adnan al-Zurfi na da kwanaki 30 ya kafa gwamnati kuma dole sai ya samu amincewar majalisar dokokin Iraqi mai kujeru 329. Sai dai kuma tuni  'yan shi'a suka nuna cewa nadin na shi ba wani abin a yaba ba ne.