'Yan Siriya miliyan uku ne ke yin gudun hijira
August 29, 2014Talla
Shugaban hukumar Antonio Guterres ya ce wannan addadi da aka samu shi ne mafi yawa da aka taɓa gani a wannan zamani inda ya ƙara da cewar a shekarar da ta gabata kadai mutum miliyan guda ne suka tsere daga ƙasar sakamakon rikicin da ake yi.
Ƙaruwar yawan 'yan gudun hijirar na Siriya dai na zuwa daidai lokacin da 'yan ƙungiyar nan ta IS ke ci gaba da rajinsu na kafa daular Musuluci, lamarin da ya sa ake ganin yawan wanda za su kaurace wa ƙasar zai iya ƙaruwa nan gaba.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane