1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Siriya ne za su iya warware rikicinsu - Brahimi

August 20, 2012

Sabon manzon Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen larabawa kan rikicin Siriya Lakhdar Brahimi ya ce al'ummar Siriya ce kaɗai za ta iya taimakawa wajen kau da rikicin ƙasar.

Nordrhein-Westfalen/ ARCHIV: Der damalige Sonderbeauftragte der vereinten Nationen fuer Afghanistan, Lakhdar Brahimi beantwortet auf einer Pressekonferenz nach der Aussenministerkonferenz "Afghanistan im Wiederaufbau" auf dem Petersberg in Bonn die Fragen der Journalisten (Foto vom 02.12.02). Eine Woche nach dem Ruecktritt von Kofi Annan als UN-Sondergesandter fuer Syrien wird der fruehere algerische Aussenminister Lakhdar Brahimi als aussichtsreicher Kandidat fuer die Nachfolge gehandelt. (zu dapd-Text) Foto: Torsten Silz/dapd
Lakhdar BrahimiHoto: dapd

Lakhdar Brahimi ya ce rikicin na Siriya wanda ya dagule zai zo karshe ne kawai in har al'ummar kasar da ma masu riƙe da madafun iko sun maida hankali a kan warware shi ta hanyar laluma maimakon afmani da tsinin bindiga wajen cimma burinsu.

Mr. Brahimi ya yi wannan furuci ne a ƙarshen mako dangane da yadda ya ke kallon lamarin da ma dai dabarun da ya kamata a ce an yi amfani da su wajen kawo ƙarshen zubar da jinin da ya ƙazanta a ƙasar biyo bayan rajin da 'yan adawa na Syrian National Council ko SNC a taƙaice ke yi na ganin sun raba shugaba Bashar al-Assad da gadon mulki.

Ya ce "al'ummar Siriya ne za su kawo zaman lafiya a Siriya, a ƙarshe dai ba mai shiga tsakani ba ne ko kuma kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ne za su samar da zaman lafiya a ƙasar, al'ummar ta Siriya ne da kansu za su samar da zaman lafiya".

Hoto: Reuters

Shakkun 'yan adawa game da warware rikicin

To duk da cewar mazon na musamman ya yi waɗannan kalamai, da dama musamman ma dai masu fashin baƙi kan rikincin na Siriya da batun warware shi na ganin da wuya idan tarihi ba zai maimaita kansa ba game da gaza cimma daidaito tsakanin gwamnatin Assad da 'yan adawa kasasncewar tun tafiya ba ta yi nisa ba 'yan adawar sun fara nuna shakkunsu kan Mr. Brahimi din saboda kalaman da su ka ya yi da ke nuna cewar lokaci bai yi ba da za a ce shugaba Assad ya yi murabus, sai dai Mr. Brahimin ya ce 'yan adawar sun yi wa kalaman na sa mummunar fahimta.

Sakamakon wannan fahimta su 'yan adawar su ka yi wadannan kalaman na Mr. Brahimi ne da ya sanya 'yan adawar kin amincewa da su hau tebirin da tattaunawa da shi domin duba yadda za a kashe wutar rikicin cikin ruwan sanyi.

Janar Babacar GayeHoto: picture-alliance/dpa

Ƙarewar wa'adin dakarun Majalisa Ɗinkin Duniya da ƙalubalen da su ka fuskanta

Wannan turka-tarkar da ke wanzuwa tsakanin manzon na Majalisar Ɗinkin Duniyar da 'yan adawar ta Siriya dai na zuwa ne daidai lokacin da aikin dakarun da Majalisar ta Ɗinkin Duniyar ta aike ƙasar domin sanya idanu kan rikicin na Siriya ya zo ƙarshe a yau litinin, aikin da da jama'a da dama ciki har da madugun masu sanya idanun Janar Babacar Gaye ke ganin ya gamu da ƙalubale da dama wanda ya sanya su gaza cimma wani abu na a zo a gani.

Ya ce "ko shakka babu mun ci karo da kalubale kasancewar ɓangarorin biyu basu bi tsarin da aka gidaya sau da ƙafa ba".

To sai dai duk da cewar sun fuskanci koma baya game da aikin na su da ma dai ire-iren kalubale da su ka fuskanta, Janar Gaye ya ce abin farin cikin shi ne Majalisar Ɗinkin Duniya za ta cigaba da kasancewa a ƙasar lamarin da ya shi ganin akwai yiwuwar cimma nasara nan gaba.

Ya ce "kwanciyar hankali na ɗaya ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya za ta cigaba da kasancewa a ƙasar, ko ma waye zai tafi ko kuma zai cigaba da kasancewa a ƙasar abun da ke da muhimmanci shi ne Majalisar Ɗinkin Duniya na nan kuma za ta cigaba da dagewa wajen ganin kawo ƙarshen rikicin da ma dai dagewa wajen ganin an yi sulhu tsakanin ɓangarorin biyu".

Faɗa ba ya hana Assad ibadaHoto: Reuters

Abin jira a gani dai shi ne irin kamun ludayin da Majalisar Ɗinkin Ɗuniya za ta yi game da cimma wannan nasara da aka sanya a gaba gami da irin kamun ludayin Lakhdar Brahimi na shiga tsakani da nufi wanzar da zaman lafiya a ƙasar ta Siriya wadda riki ya ɗaiɗaita.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi

Za a iya sauraron wannan rahoton daga nan ƙasa