1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan siyasar Jamus sun caccaki Musk kan AfD

Abdullahi Tanko Bala
December 20, 2024

Bayan da Elon Musk ya wallafa goyon bayansa ga Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus, manyan 'yan siyasar kasar sun soki lamirinsa da yin katsalandan ga zaben kasar da ke tafe.

Elon Musk
Hoto: Evan Vucci/dpa/picture alliance

Elon Musk ya haifar da dambarwar siyasa a Jamus bayan da ya baiyana Jam'iyar AfD mai akidar kyamar baki da cewa ita ce kadai za ta iya ceo Jamus daga halin da ta shiga.

Elon Musk ya baiyana hakan ne a shafinsa na X da ya saya a shekarar 2022.

Jami'yyar AfD ita ce ta zo ta biyu a kuri'ar jin ra'ayin jama'a a Jamus da kashi 19 cikin dari, watanni biyu gabanin zaben da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2025

Sai dai kuma dukkan sauran jam'iyyun kasar sun ce ba za su yi kawance da ita ba.

Manyan 'yan siyasar Jamus sun soki Musk dangane da goyon bayan da ya nuna wa Jam'iyyar ta AfD mai akidar kyamar baki da cewa katsalandan ne a siyasar kasar gabanin zaben da ke tafe.