'Yan ta'adda sun hallaka sojojin Nijar a Dosso
May 7, 2025
Hukumomin kasar a cikin wata sanarwa da aka watsa a gidan rediyon gwamnati, ne suka sanar da haka, yayin da wata majiya ta tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa adadin mutanen da aka kashe na iyazarta haka.
Sanarwar ta gwamnati ta danganta harin na kwanton bauna da aka kai a kudancin Nijar ranar Litinin ga "'yan ta'adda” tare da bayyana cewa an kashe wasu daga cikin maharan kuma an kama wasu.
Majiyar tsaro ta ce sojoji 18 ne suka bace. Haka kuma, an sace motocin tsaro guda uku, a yayin harin. Gwamnati ta bayar da umurnin hana amfani da babura a cikin al'ummomin da abin ya shafa.
Jamhuriyar Nijar tare da makwabtanta na kasashen Sahel kamar Mali da Burkina Faso sun dauki dogon lokaci suna yaki da 'yan tawaye na kungiyoyin jihadi da ke da alaka da Al Qaeda.