1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe fararen hula 11 a yankin yammacin Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Moh' Abubakar
October 23, 2022

Wasu 'yan bindiga a yankin yammacin Nijar sun kashe fararen hula fiye da 10 a Banibangou da ke jihar Tillaberi mai iyaka da Mali da Burkina Faso.

Sojojin Jamhuriyar Nijar a fagen daga
Sojojin Jamhuriyar Nijar a fagen daga Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Rahotanni na cewa harin ta'addancin ya halaka mutane 11 a yankin mai iyaka da Mali da Burkina Faso. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wani jami'in gwamnati na cewa an maharan dauke da makamai sun far wa wasu motoci uku ne, kuma nan take suka kashe mutane tara da ke cikin, kana daga baya sun kara kashe wasu mutane biyu da ke kan babur a kauyen Tizigorou a gundumar Banibangou da ke yammcin kasar.

Ba tun yau ba dai kasar Nijar ke fama da hare-haren 'yan bindiga musamman ma yankunanta da ke makwaftaka da mali da Burkina Faso, lamarin ya yi sanadiyar salwantar dumbin rayuka da asarar dukiyoyi.