1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Hare-hare sun ritsa da farar hula

Abdourahamane Hassane
July 16, 2023

Rundunar Sojojin Nijar ta ce an kashe wani jandarma da fararen hula hudu a wani harin ta'addanci da aka kai kan hanyar Torodi zuwa Makalondi, a yankin Tillabéri da ke kudu maso yammacin kasar kann iyaka da Burkina Faso.

Niger Symbolbild Fahne | Gedenken
Hoto: Boureima Hama/AFP

 

A cikin wata sanarwa da rundunar ta bayyana, ta ce  wasu yan taadda sun kai hari a kan wani rukunin jami'an jandarma na kasa a wani ayarin motocin rakiya a yankin Torodi-Makalondi. A cewar rahoton, mutane biyar suka mutu ciki har da wani jandarma da fararen hula hudu.Yayin da mutane 19 suka jikkata da suka hada da jandarmomi bakwai da sojoji biyar da fararen hula bakwai wadanda tuni aka kaisu asibitin a yamai. A bangaran yan ta'Aaddar kuma an kashe mutum biyu tare da kwace musu wasu makamai da babura guda biyu. Yankin na tilaberi da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Burkina da Mali a kudu maso yammacin kasar, na yawan fuskantar hare-hare na 'yan ta'adda.