'Yan ta'adda sun kai hari birnin Bamako
April 25, 2026
A sanarwar da sojojin suka fitar, 'yan ta'addan da ba a kai ga tantance su ba sun yi yunkurin kai hari a wasu muhimman wurare gami da barikin soji.
Rahotoni sun tabbatar da gwabza fada a Bamako da Gao da Kidal da ke arewacin kasar da kuma tsakiyar birnin Sevare.
Mazauna anguwar Kati dake tsakiyar Bamako sun bayyana inda shugaban mulkin sojin ke zama sun bayyan jin karar harbin bindiga da ma wallafa yadda harbin ya lalata wasu gidaje.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren. Sai dai tuni masu ikirarin jihadi suka yi kokarin gurgunta babban birnin kasar a bara ta hanyar katse man da yake samu.
Kasar Mali dake yankin yammacin Afirka ta kwashe sama da shekaru 10 tana fama da ayyukan mayakan jihadi.
Karin BayaniKungiyar JNIM ta sake kai wa tankokin mai hari a Mali: