1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ta'addanci na gigita fararen hula a Nijar

Binta Aliyu Zurmi Abdoulaye Mamane
December 15, 2024

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun kai wasu hare-haren da suka kashe fararen hula 39 ciki har da mata da kananan yara a kauyukan Libiri da Kokorou na jihar Tera mai iyaka da kasar Burkina Faso.

Bataliyar sojojin Nijar na sintirin yaki da ta'addanci
Bataliyar sojojin Nijar na sintirin yaki da ta'addanciHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Ma'aikatar tsaro a Nijar ta sanar da wasu hare-haren 'yan bindiga da suka hallaka akalla mutane 39 a yankin yammacin kasar da ke da iyaka da Burkina Faso.

A cikin sanarwar da ma'aikatar tsaron Nijar ke fitarwa sau biyu a mako, hukumomin Nijar din sun kara da cewar tagwayen hare-haren da aka kai a garin Libiri ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane 21 yayin da a garin Kokorou aka kashe wasu 18 ciki har da mata da kananan yara, sai dai gwamnatin ba ta bayyana takamaiman lokacin da aka kai harin ba, to amma sojojin na Nijar sun ce an kai su ne a tsakanin ranakun 12 zuwa 14 na wannan wata.

Karin bayani:  Sojoji sun musanta kisan dakarunsu a Nijar

Hukumomi a yankin Tera mai iya da Burkina Faso daga yammacin Nijar, sun nuna alhini ga iyalan mamatan wadanda dama ke cikin jimamin mutuwar mutane 21 da suka mutu a yayin wani harin ta'addanci da aka kai kan motocin dakon kaya masu dauke da fararen hula a makon jiya.

Karin bayani: Takaddamar Orano da gwamnatin Nijar

Yankunan da ke kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da ke kan iyakokin juna sun jima suna fama da ayyukan 'yan ta'adda da ke da alaka da kungiyoyin Al-Qaid da ta IS, hare-haren da suka kashe dimbin fararen hula, a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen ke kokarin kawar da mayakan jihadi da ke yi wa al'ummominsu illa.