'Yan ta'adda sun kashe mutane 26 a Kenya
June 16, 2014Rahotanni daga birnin Mombasa na kasar Kenya, sun ce akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin da wasu gungun mutane akalla 50, dauke da makammai suka kai a yammacin jiya Lahadi har ya zuwa kusan wayewar wannan Litinin din (16.06.2014), a birnin Mpeketoni dake yammacin kasar ta Kenya.
Da yake magana wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP a yau Litinin, mataimakin Shugaban gundumar ta Mpeketoni Benson Maisori, ya ce kawo yanzu dai sun samu tattara gawarwakin mutane akalla 26, inda suka ajiyesu a dakunan ajiyar gawarwaki, kuma suna ci gaba da neman wasu.
Sai dai kuma a wani adadin da jami'an tsaron 'yan sanda suka bayar, sun ce mutane 14 ne suka rasu, wasu kuma fiye da ashirin suka ji rauni, a cewar kakakin 'yan sandar yankin.
Maharan dai da ake dagantawa da 'yan kungiyar al-Shabab na kasar Somaliya, sun jima ana dauki ba dadi da su a wannan birni na Mpeketoni, inda suka yi kaca-kaca da muhimman gine-gine a birni. Sai dai kuma kura ta lafa a wannan Litinin din.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe