1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso:'Yan bindiga sun kashe mutum 160

Abdourahamane Hassane
June 6, 2021

Hukumomi a Burkina Faso sun ce addadin mutane da 'yan bindiga suka kashe a harin da suka kai a karshen mako a Salhon da ke a  yankin arewa maso gabashi kasar ya  kai mutum 160.

Burkina Faso Symbolbild Anschlag
Hoto: Str/AFP

Yanzu haka dai an yi jana'izar mutanen, wadanda suka hada da mata da yara da maza  wadanda aka yi wa bisar jam'i a cikin manyan ramuka guda uku. Babu dai wata kungiya kawo yanzu da ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin, sai dai ana kyautata zaton cewar masu  jihadi ne suka kai harin. Wannan shi ne hari mafi muni da 'yan ta'addar suka kai a Burkina Faso tun bayan harin da ya afku a shekara ta 2015 wanda a ciki mutane 30 suka mutu galibi 'yan kasahen waje.