1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojoji Nijar 23 a yakin Tillaberi

Mouhamadou Awal Balarabe
March 22, 2024

Gwamnatin sojan Nijar ta ce kwantan bauna da masu ikirarin jihadi suka kai a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso da Mali ne ya yi sanadin mutuwar dakarunta. Amma sojojin sun yi nasarar kame 'yan ta'adda kusan talatin,

Sojojin Nijar na tinkarar 'yan ta'adda gadan-gadan
Sojojin Nijar na tinkarar 'yan ta'adda gadan-gadanHoto: Mads Claus Rasmussen/Ritzau Scanpix/picture alliance

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sanar da mutuwar dakarunta 23 a kwantan bauna da masu ikirarin jihadi suka kai a yankin da ke kusa da iyakar kasar da Burkina Faso da Mali. Wannan sabon harin ya faru ne a lokacin da sojojin ke sintiri a cikin wannan mako don dakile ayyukan ta'addanci a yankin Tillabéri, wanda ya ba su damar kame 'yan ta'adda kusan talatin, a cewar sanarwar da ma'aikatar tsaro ta fitar a birnin Yamai.

karin bayani:Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar

Tun shekarun bakwai da suke gabata ne yankin Tillabery ya zama maboyar masu ikirarin jihadi ciki har da Al Qaeda, inda ake fama da hare-haren kungiyoyi da ke dauke da makamai, duk da dimbin dakarun da ke jibge a wannan yanki. Ko da a karshen watan Janairu, an kashe fararen hula 22 a wani hari da aka kai a kauyen Motogatta da ke cikin gundumar Tondikiwindi mai nisan kimanin kilomita dari da babban birni Yamai.

Karin bayani: Rundunar tsaron hadin gwiwa a kasashen AES

Tun a karshen watan Yulin 2023 ne, Jamhuriyar Nijar ta koma karkashin jagorancin sojoji da suka karbe mulki domin a cewarsu su dakile tashe-tashen hankulan da 'yan ta'adda ke haddasawa, amma ana ci gaba da kai hare-hare nan da can.