1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojoji sa kai a Nijar

Abdul-raheem Hassan
February 27, 2026

Rahotanni daga majiyoyin cikin gida daga yammacin jamhuriyar Nijar, sun ce ‘yan ta’adda sun kashe jami'an sa kai da ke taimaka wa sojojin gwamnati 25 a wasu kauyuka da ke kusa da kan iyaka da kasar Mali.

Wani sojan Nijar a fagen daga
Wani sojan Nijar a fagen dagaHoto: Ludovic Marin/AFP

Wani tsohon magajin garin Anzourou ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, " ‘Yan bindigar dauke da manyan makamai, sun yi wa sojojin sa kai 25 kwnatan bauna a yankin Tillaberi wani yanki mai fama da kungiyoyin jihadi."

Wani sheda na dabam da ya tabbatar da harin ya ce"Akwai matasa masu kare kansu 25 da suka rasa rayukansu da kuma wasu uku da suka samu raunuka. An kwashe su zuwa asibitoci a garin Tillaberi da Yamai." Yankin Tillaberi wani yanki ne a Nijar da ke fama da ayyukan kungiyar jihadi ta IS reshen Sahel.

Majiyar kungiyar ta ce wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka hudu da ke makwabtaka da su kamar Doukou Makani da Doukou Djinde da Doukou Saraou da kuma Doukou Koirategui. Gundumar Anzourou tana da kusan kauyuka 50 da kauyuka a cikin Tillaberi mai iyaka da yankin da ke tsakanin Nijar da Burkina Faso da kuma Mali, inda aka dade ana kai munanan hare-haren 'yan jihadi.

Kungiyar ACLED mai mai sa ido kan ayyukan ta'addanci a Nijar, ta ce a shekarar 2025, yankin Tillaberi ya zama yanki mafi muni a tsakiyar Sahel, inda sama da mutane 1,200 suka mutu. Kungiyar ta dora alhakin tashe-tashen hankula a kan kungiyar IS da ke yankin Sahel, sai kuma sojojin Nijar da kungiyar Al-Qaeda mai alaka da goyon bayan Musulunci da Musulmai (JNIM).

Jamhuriyar Nijar na karkashin mulkin soja tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023. A cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar ta fuskanci munanan hare-haren masu jihadi. Tun farkon shekara, an sami mutuwar kusan 2,000, a cewar kungiyar ACLED.

Yayin da sojojin Nijar ke fafutukar ganin sun dakile hare-haren, sun hakura da samar da dakarun kare kai da mazauna kauyuka suka yi, lamarin da ya kai ga kazamin fada da masu jihadi. A cikin watan Disamban shekarar 2025, gwamnatin mulkin soja a Yamai ta sanar da shirin neman hadin kan jama'a da dukiyoyinsu domin yakar masu kishin Islama.

Jamhuriyar Nijar ta kafa rundunar hadin gwiwa mai dakaru 6,000 tare da Mali da Burkina Faso, kasashen da kuma ke karkashin sojojin da ke fuskantar tashin hankalin masu jihadi.