1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar

July 5, 2025

Wasu hare-hare biyu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai a kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji 10, yayin da hukumomi suka bayyana cewa an kashe ‘yan ta'adda 41 a wannan hari.

Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Ministan Tsaro a Nijar Janar Salifou Modi ya bayyana a wata sanarwa cewa hare-haren da aka kai a lokaci guda daga da ke kama da na "mayakan haya” ya faru ne a garuruwan Bouloundjounga da Samira da ke sashen Gotheye.

Sanarwar, wadda aka karanta a talabijin na kasa, ta ce an kashe sojoji 10 sannan wasu 15 sun ji rauni.

Akwai ma labarin da ya nuna cewa bangaren maharan ma, an salwantar da mutane 41.

Sashen Gotheye yana kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso, kuma an dade ana samun hare-haren ‘yan jihadi a wannan yanki.

Garin Samira dai na dauke da kamfanin hakar zinariya na masana'antu na farko a Nijar.