1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Tsohuwa ta tsira

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

Rahotanni daga Ouagadougou babbar birnin Burkina Faso, na nuni da cewa masu da'awar jihadi sun sako malamar Cocin nan 'yar kasar Amirka mai kimanin shekaru 83 da suka sace a arewacin kasar.

Burkina Faso | Sojoji | Hari
Sojojin Burkina Faso na fama da yaki da 'yan ta'addaHoto: Michel Cattani/AFP

Cikin watan Afirilun wannan shekara da muke ciki ne dai, 'yan ta'addan suka sace Sister Suellen Tennyson da ke aiki a Congregation of Marianites of the Holy Cross tun daga shekara ta 2014.  Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa Cocin mabiya darikar Katolika ta kasar sanar da cewa, mayakan sun sako ta kuma a yanzu tana tudun mun tsira. Burkina Faso dai, na daga cikin kasashen da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin Afirka ta Yamma.