1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

An kammala yakin neman zabe a Kamaru

Abdourahamane Hassane
October 11, 2025

A gobe Lahadi ake gudanar da zaben shugabnan kasa a Kamnaru bayan kammala makwani uku na yakin neman zabe.

Hoton  Paul Biya
Hoton Paul Biya Hoto: AFP

'Yan takara 12 za su fafata a zaben a ciki har da  shugaban mai barin gado Paul Biya  wanda yake kan karagar mulki tun a shekarea ta 1982, wanda ke da shekaru 92 da haifuwa.

Yanzu haka dai abokin aikina Mohammad Awal Balarabe yana a birnin  Yaounde wanda ya je don zaben kuma ya shai mana cewar ya zuwa yanzu an kammala yakin neman zabe.