1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan takarar shugaban kasa a Senegal sun fara yakin zabe

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 9, 2024

A baya dai an tsara gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata, amma sai shugaba Macky Sall ya dage zaben, lamarin da ya jefa kasar cikin rudani da tashin hankali

Hoto: Stefan Kleinowitz/AP/picture alliance

'Yan takarar shugaban kasa a Senegal sun kaddamar da yakin neman zabe a Asabar din nan, biyo bayan makonni da aka shafe ana fuskantar tashin hankali a kasar bayan dage zaben.

Karin bayani:Senegal: Sabuwar ranar zabe daga kotu

'Yan takarar da aka amince su shiga zaben su 19, suna da gajeren lokacin yakin neman zaben, wanda za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Maris, da ake kyautata zaton zai yi zafin da ba a taba ganin irin sa ba tun bayan samun 'yancin kasar, yau sama da shekaru 60.

Karin bayani:Senegal: Za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yuni

A baya dai an tsara gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata, amma sai shugaba Macky Sall ya dage zaben, lamarin da ya jefa kasar cikin rudani da tashin hankali.