SiyasaAfirka
'Yan takarar shugaban kasar Mauritania na karkare yakin zabe
June 28, 2024![](https://static.dw.com/image/69367625_800.webp)
Talla
A Juma'ar nan ce 'yan takarar shugaban kasa a ke karkare gamgamin yakin tallata manufofinsu, domin tunkarar zaben da za a gudanar a gobe Asabar.
Karin bayani:Mauritania
To sai dai shugaban kasar Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani ya ce babu makawa shi zai sake lashe zaben, domin samun wa'adin mulki na biyu.
Karin bayani:MDD na fargabar fantsamar rikicin kasashen Sahel zuwa makwabta
'Yan takara bakwai ne ciki har da shugaba mai ci ke takarar zaben, a wannan kasa mai fama da hare-haren ta'addancin masu ikirarin jihadi.