'Yan tawaye a Iraki sun ƙwace iko da birnin Mossul na Iraki
June 10, 2014Talla
Firaministan ya yi wannan kira ne bayan da masu kaifin kishin addini suka ƙwace iko da birnin wadda ke a arewacin ƙasar.
Jihar ta Ninive da ke a yankin arewaci wadda birnin Mossul mai arzikin man fetur shi ne babban birninta, inda 'yan sunni ke da rinjaye wanda shi ne birni na biyu mafi girma. Shugaban majalisar dokokin ƙasar ya ce masu kishin addinin na kan hanyarsu ta ƙwace iko da jihar Salaheddine da ke a kudanci inda ba a yi wani kataɓus ba. Wannan shi ne karon farko da 'yan tawye na Iraki galibi 'yan shi'a masu fafutukar ganin an kafa daular islama suka ƙwace iko da birnin guda sukutum.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman