1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawaye sun kai hari a ƙasar Mali

May 11, 2007

Rahottani daga ƙasar Mali, sun ce wani ayarin abzinawa ɗauke da makamai, da su ka zo daga Jamhuriya Niger, da Mali, sun kai hari ga cibiyar jami´an tsaro, da ke Tinza, a yankin Kidal, kussa da iyaka da Algeria.

Wannan shine hari mafi girma da abizanawa yan tawaye su ka kai, a ƙasar tun bayan yarjejniyar sulhu da aka rattaba hannu kan ta, a ƙasar Algeria ranar 4 ga watan juli na shekara da ta gabata.

Ƙungiyar tawayen da Ibrahim Bahanga ke jagoranta, ta ɗauki alhakin kai wannan hari, wanda ya zuwa yanzu, a ba tantance sakamakon assara da ya jawo ba.

Saidai gwamantin Bamako, ta tura ƙarin jami´n tsaro, a yankin da abunya faru.

Ƙasar Mali, na ɗaya daga ƙasashen Afrika kudanci Sahara da ke fama da rikicin tawaye.