1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun kai hari kan soja a Mali

June 3, 2025

Kungiyar tawaye da ke da alaka da Al Qaeda a kasar Mali, ta dauki alhakin wani hari da aka kai wata cibiyar sojoji a ranar Lahadin da ta gabata.

Sojojin gwamnatin kasar Mali
Sojojin gwamnatin kasar MaliHoto: Getty Images/AFP/J. Saget

Kungiyar Jama'a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin watau JNIM a takaice, ta ce ta karbe iko da sansanin soji na Boulkessi da ke tsakiyar Malin, iyaka da Burkina Faso.

Sama da sojoji 30 ne dai suka salwanta a harin da sojoji suka ce an tilasta musu janyewa aka yi a lokacin.

Kungiyar ta JNIM ta kuma ma dauki alhakin hare-hare da dama a baya-bayan nan a yankin na Mali.

Ko a ranar 24 ga watan jiya ma dai ta ce ita ta kai hari a sansanin soji na Dioura inda sojoji 40 suka mutu.

A ranar Juma'a ma dai ta kwace wani sansanin na soji a Sirakorola a kudu maso yammaci, amma kuma dakarun kasar suka kwace.

Sama da sojoji 400 ne dai suka mutu a watan jiya sakamakon ayyukan ta'adda a kasashen Mali da Nijar da ma Burkina Faso.