1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fada ya rincabe a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Suleiman Babayo ZUD
October 22, 2024

A kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango 'yan tawaye sun musanta ikikarin dakarun gwamnati na sake kwace garin Kalembe mai tasiri na gabashin kasar, inda ake fama da tashe-tashen hankula da suka raba mutane da gidajensu.

Kwango | Sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a garin Goma
Sojojin kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

A wannan Talata sojojin kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun bayyana sake kwato garin Kalembe na gabashin kasar da 'yan tawayen kungiyar M23 suka kwace kwana guda da ta gabata, amma har yanzu ana cikin yanayin tararrabi.

Ranar Lahadi da ta gabata 'yan tawayen suka kwace garin kafin daga bisani sojojin gwamnati da magoya bayan su masu dauke da makamai suka sake kwace garin.

Kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta kwashe shekara da shekaru tana fama da tashe-tashen hankula na kungiyoyin 'yan tawaye musamman a yankin gabashin kasar mai albarkatun ma'adanai inda yanzu haka kimanin mutane milyan 2.6 suke rayuwa a mastayin 'yan gudun hijira.