1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

`Yan tawayen Chadi sunce dakarun da zaa tura abokan gabarsu ne

November 30, 2007

Yan tawaye na ƙasar Chadi sun ce za su ɗauki dukkanin dakarun ƙetare da a ke shirin turawa ƙasar karkashin Ƙungiyar Taraiyar Turai a matsayin abokan gaba.Ƙungiyar ta UFDD cikin wata sanarwa ta ce yanzu haka dai ta yanke cewa tana cikin yaƙi ne da dakarun Faransa da ma duk wasu rundunoni da ke cikin ƙasar.Tuni aka tura dakarun Faransa da jiragen yaƙi zuwa Chadi ƙarƙashin wata yarjejeniyar tsaro tsakaninsu.Dakarun na EU waɗanda yawancinsu daga Faransa za a ɗauka ana shirin tura su ne zuwa gabacin Chadi kusa da bakin iyakarta da Sudan domin kare yan gudun hijira da maaikatan agaji.Shugaban Faransa Nicolas sarkozy ya yi watsi da barazanar yan tawayen yana mai cewa barazanar ba zata yi tasiri ga shirinsu na tura dakarun EU zuwa Chadin ba.