1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan tawayen Houthi harba manyan makamai a Tekun Maliya

January 31, 2024

'Yan tawayen Houthi a Yemen na i gaba da bayyana cewa sun kai wasu hare-haren manyan makamai a kan jiragen ruwan Amurka a kan teku, daidai lokacin da Amurka da Burtaniya ke martani.

Wani jirgin ruwa da 'yan Houthi suka kai wa hari a Bahar Maliya
Wani jirgin ruwa da 'yan Houthi suka kai wa hari a Bahar MaliyaHoto: Indian Navy/AP/dpa/picture alliance

'Yan tawayen Houthi a kasar Yemen, sun harba makamai masu linzami da dama kan jiragen yakin Amurka a tekun Bahar Maliya.

Wannan dai na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan Amurka ta sanar da cewa ta kakkabo wani makami mai linzamin.

Cikin watanni da suka gabata dai, mayakan na Huthi da ke adawa da kasashen yamma da Isra'ila, sun tsananta farmaki a kan jiragen ruwa na kasashen duniya.

Hakan ya janyo turjiya daga sojojin Amurka da Burtaniya musamman, wadanda ke kai hare-hare na martani.

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon a Amurka, ta ce mayakan tawayen sun kaddamar da hare-hare fiye da 30 a kan jiragen ruwan, tun bayan fara farmakin a ranar 19 ga watan Nuwambar bara.