1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan tawayen Houthi na Yemen sun harbo jirgin yakin Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 16, 2024

Mai magana da yawun kungiyar Yahya Saree, ya bayyana sunan jirgin da suka harbo da MQ-9 Reaper drone kirar Amurka

Hoto: U.S. Air Force/AP/picture alliance

'Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi ikirarin kakkabo wani jirgin Amurka marar matuki a Litinin din nan, inda wani faifan bidiyo ya nuna yadda suka harba makami mai linzami har ya harbo jirgin, sannan hayaki ya turnuke bayan tarwatsewarsa a yankin Dhamar.

Karin bayani:Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen

To sai dai Amurkan ba ta ce komai ba game da wannan ikirari na Houthi.

Karin bayani:Amurka ta kai sabbin hare-hare kan Houthi a Yemen

Mai magana da yawun kungiyar Birgediya Janar Yahya Saree, ya ce sunan jirgin da suka harbo MQ-9 Reaper drone, kirar Amurka.