1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Libiya sun gamu da cikas

August 13, 2011

'Yan tawayen Libiya dake fafatawa da gwamnatin Gaddafi, sun samu asara, inda aka raunata aƙalla 50 yayinda wasu da dama suka mutu biyo karawa da dakarun gwamnati.

'Yan tawayen Libiya a fagen daga na fafatawa da sojin gwmanatin Gaddafi a kusa da BuregaHoto: dapd

'Yan tawayen ƙasar Libiya sun yi muguwar asara a yunƙurinsu na kame tashar jiragen ruwa da kuma matatar mai dake birnin Burega. Ma'aikatan lafiya a asibitin garin Ajdabiya da ke kusa da Burega, sun bayyana cewa aƙalla 'yan tawayen 50 aka kawo asibiti, yayin da wasu 11 suka ta fi lahira, bayan da ƙwararrun dakarun gwamnatin Libiya suka yi wa 'yan tawayen ƙofar rago. 'Yan tawayen dai sun sanar da cewa sun kame birnin na Burega tun kwanaki, amma suna kilomita 15 daga tashar jiragen ruwa da kuma matatun mai. Sai dai muƙaddashin ministan tsaron Libiya Khalid Kaim, ya ce ƙarya ce kawai 'yan tawayen suka baza, ba su ma shiga birnin balle neman isa tashar, kana Kaim yace yawan 'yan tawayen da aka she sun kai 20. 'Yan tawayen Libiya sun sha yunƙurin kame tashar jiragen ruwan domin samun hanyar fitar da mai zuwa waje, wanda zai iya tallafa musu, a burin da suke yi na kawar da gwamnatin Gaddafi, wanda ya gagaresu watanni shida kawo yanzu, duk da luguden wutar da dakarun NATO ke kaiwa ta sama da 'yan tawaye a ƙasa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal