'Yan tawayen Siriya na barazanar kaurace wa tattaunawar
January 3, 2017![Syrien Damaskus Wasserkrise IS blockiert Wadi Barada](https://static.dw.com/image/36981669_800.webp)
Talla
'Yan tawayen dai sun yi wannan barazana ce, dangane da abun da suka kira kin mutunta yarjejeniyar daga bangaran dakarun Gwamnatin Shugaba Bahar Al-assad. Su dai 'yan tawayen sun ce sun yi biyayya ga yarjejeniya, amma kuma bangaran dakarun gwamnati da masu mara musu baya, na ci gaba da take taka ta musamman ma a yankunan Wadi Barada da kuma Ghouta ta Gabas da dukanninsu ke cikin jihar Damaskus babban birnin kasar ta Siriya.
A cewar kungiyar da ke sa ido kan kare hakin bil -Adama a kasar ta Siriya, dakarun gwamnati da mayakan Hezbollah 'yan Shi'a na kasar Lebanon da ke mara musu baya, sun ci gaba a wannan Talata da samaman da suke kai wa a yankunan da ke a nisan km 15 da birnin na Damaskus.